Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya sanar da ƙaƙaba dokar hana fita a jihar bayan zanga-zangar nuna fushi kan matsin rayuwa ta rikiɗe zuwa rikici.

Gwamnan ya bayyana haka ne a wani taron manema labaru da ya gudanar yau a Kano.

Zanga-zangar ta rikiɗe zuwa tarzoma ne bayan wasu matasa sun fara afka wa wuraren ajiye abinci suna wawashewa.

Hakan ya haifar da arangama tsakanin masu zanga-zangar da jami’an tsaro.

A cikin bayanin nasa, gwamnan na Kano, Abba Kabir ya ce: “A taron tsaro na gaggawa da muka gudanar da shugabannin hukumomin tsaro a jihar Kano, gaba ɗayanmu mun yanke shawarar ƙaƙaba dokar hana fita ta awa 24 domin ganin an dawo da doka da oda.”

Wasu daga cikin masu zanga-zanga sun ɓalle wuraren ajiye kayan abinci, inda suka kwashe buhunan shinkafa, kwalayen taliya da kuma man girki.

A ranar Laraba Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya nemi masu zanga-zangar da su guji tashin hankali, har ma ya gayyace su zuwa gidan gwamnati domin kai ƙorafinsu.

“Ina tabbatar muku cewa gwamnati ba za ta lamunci irin waɗannan ayyukan ba,” in ji shi yayin da yake yi wa ƴan kasuwa da sarakunan gargajiya, da malaman addini jawabi a gidan gwamnati.

“Maimakon haka, ina miƙa goron gayyata ga masu son yin zanga-zanga da su zo gidan gwamnati, inda zan ji daɗin sauraren koke-kokensu kuma mu gudanar da tattaunawa mai ma’ana.”

Waɗanne yankuna lamarin ya fi shafa a Kano?

Kano
Bayanan hoto,Wasu ɓata-gari sun fasa shaguna a birnin Kano lokacin da ake gudanar da zanga-zangar a kan titin State Road

Titin zuwa gidan gwamnatin Kano da aka fi sani da State Road, shi ne wuri na farko-farko da ya fara shaida fushin matasan, inda suka farfasa duk abubuwan da suka gani a gefen titin.

Wasu masu zanga-zangar sun fasa wani shagon sayar da kaya tare da yashe kayayyakin da ke cikinsa. Sai dai ‘yansanda sun harba musu hayaƙi mai sa hawaye.

“Duk wanda ya san wannan titi ya sani cewa a tsare yake amma yanzu an yamutsa wurin gaba ɗaya,” in ji wakilin BBC a Kano Zahraddeen Lawan.

A gefe guda kuma, ‘yansanda sun bi sun ƙwato wasu daga cikin kayayyakin da aka kwashe kuma suka tara su wuri guda.

Kazalika, matasan sun auka wa katafaren ginin nan na Digital Industrial Park da ke cikin sakatariyar Audu Bako. Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta gina shi da zimmar horar da matasa game da harkokin sadarwa da kuma ƙirƙirarriyar fasaha. Rahotonni na cewa a mako mai zuwa ne ake sa ran ƙaddamar da shi.

Hotouna da bidiyo da aka wallafa a shafukan zumunta sun nuna yadda ɓata-garin suka dinga saran ƙofar ginin da makamai, yayin da wasu rahotonni ke cewa an cinna wa wani ɓangare na ginin wuta.

Ana iya jin ƙarar wani abu da ya yi kama da harbin bindiga, amma duk da haka ba su fasa yunƙurin shiga cikin ginin ba.

A gefe guda kuma, wasu na ta yunƙurin tumɓuke turaku da wayoyin da aka kakkafa a tsakiyar titin na State Road.

‘Yandaba ne aka shigo da su daga waje – Gwamnan Kano

Kamar yadda ya yi alƙawari Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya karɓi jagororin wasu ƙungiyoyi da ke zanga-zangar a gidan gwamnatinsa da ke ƙwaryar birnin.

Yayin ganawar tasu, ƙungiyoyin sun gabatar masa da ƙorafe-ƙorafensu a rubuce domin ya isar da su ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu.

Sai dai gwamnan ya zargi wasu da ya bayyana da “marasa kishin Kano” da ɗebo ‘yandaba domin shiga cikin zanga-zangar.

“Sai aka samu wasu marasa kishin Kano sun shgo mana ‘yandaba. Tun jiya muke faɗar inda suke amma sai suka ɓoye su,” a cewar gwamnan.

“Yau [Alhamis] da safe aka dinga ɗebo su a mota ana kawo su shataletale, suka hana waɗannan ƙungiyoyi nagartattu masu kishi zuwa su ba da takardu.”

Haka nan, gwamnan ya yaba wa jami’an tsaro game da “matuƙar ƙoƙarin tarwatsa su”.